http://www.hausawglwpwzr4svrerazwxt7mqpcw3hfoxp5r7jjrkttqc3qrs5syid.onion/a/messi-ya-lashe-kyautar-gwarzon-dan-kwallon-duniya-ta-shekarar-2022/6981855.html
Messi, mai shekaru 35, ya taimakawa Argentina lashe gasar cin kofin duniya da aka yi a Qatar a shekarar 2022, da kuma ya zura kwallaye 27 a wasanni 49 da ya buga wa kulob da kasar a 2021-22. The Best FIFA Football Awards 'Yar wasan Barcelona, Alexia Putellas ta zama fitacciyar 'yar wasan mata ta bana. A bikin da aka yi a birnin Paris, Lionel Scaloni, wanda ya jagoranci Argentina ta lashe gasar cin kofin duniya karo na uku, ya zama gwarzon kocin maza na bana.