http://www.hausawglwpwzr4svrerazwxt7mqpcw3hfoxp5r7jjrkttqc3qrs5syid.onion/a/rikicin-sudan-wata-sabuwar-yarjejeniyar-tsagaita-wuta-za-ta-fara-aiki/7104979.html
Majalisar Dinkin Duniya ta mayar da wasu ma'aikatanta da ayyukanta na wani dan lokaci zuwa birnin na Red Sea, bayan kazamin fada da ya barke a babban birnin kasar Khartoum, a ranar 15 ga watan Afrilu. Yarjejeniyar tsagaita wuta mai dauke da sa hannun hafsan hafsoshin sojin kasar Sudan Janar Abdel Fattah al-Burhan, da kuma dakarun kungiyar sa kai karkashin jagorancin Janar Mohamed Dagalo, za ta fara aiki da karfe 9:45 na dare. lokacin yankin a ranar Litinin, kuma yana daukar tsawon kwanaki...